WANENE SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) ???
BABI NA FARKO TARIHIN SHAIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H) A TAQAICE @Kontagara Media Forum KMF/3321/SC/002 Salsalar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) : Tarihi mafi inganci da Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayar da kansa, ya faxi cewa asali iyayensa sun fito ne daga Magrib (Moroko); Daga nan suka zo birnin Shingixi na tsohuwar daular qasar Mali, amma yanzu birnin na Shingixi mai tsohon tarihi yana qasar Mauritaniya ne, daga garin Shingixi kakanninsa suka yo qaura zuwa birnin Mabruk da ke qasar Mali, daga nan kuma suka zauna a birnin Timbuktu, daga birnin Tumbuktu ne kuma suka taho wannan qasa Nijeriya cikin qarni na 12. (Shekaru 60 Masu Albarka, shafi na 09 zuwa 11). Nasabarsa : Salsala ko nasabar Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta jero ne kamar haka; Shaikh Ibraheem xan Ya’aqub, xan Aliyu, xan Muhammad Tajuddeen, xan Liman Hussain Batoronke, shi Liman Hussain Bafulatani ne daga qabilar Toronkawa wanda ya zo qasar Hausa daga Mali a zamanin Shehu Usman bin Fodiye, inda ya zama ...