YADDA AKA GUDANAR DA ZAGAYEN MAULUDI A GARIN BABBAN RAMI



Yau Alhamis ne 12/11/2020 Al'ummar garin 


Babban Rami dake jihar Niger State, suka fito Zagayen Rally Mauludin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S A W W), domin Murnar da zagayowar Watan da aka Haifi shi.



Kamar yanda aka Saba Duk Shekara Masu zagayen sukan hada ne "Yan Darikar Tujjaniyya da Khadiriyya da "Yan Uwa Al'majiran Sheikh Ibraheem El Zakzkay (H), haka banama wannan fitowar ta hada dukkan wa yannan, Wani Abin Birgiwa da ban Sha awa ta yanda Naga Dalibban Makarantu kala daban daban kowa yasha sabun dinki mazan su da matan su yara da manya, 



A gefe Guda Kuma "Yan Uwa Al'majiran Sheikh Ibraheem El Zakzkay ne ketaka faretin Birgi Allah da Manzon sa da sauran Al'ummar Annabi ya yin da wasu ke dauke da Tutuci suna tafiya suna rera wakokin yabon Annabin Tsara Annabi Muhammad (S), Kai Abun dai yafi karfin na fada sai Wanda ya gani daga bisani akaje wajen da za a rufe Yan fareti sukayi bareti a fili sannan aka yi La anta ga kasar Faransa aka Kona Turar kasar.



An fara wannan Zagayen Lafiya Kuma Alalh da ikon sa yasa An'kammala Lafiya, ga kadan daga cikin Hotonan Muzaharar Nan da muka daukašŸ‘‡.



Kontagora Media Forum

@Shana Islam & Nusayberh Ibraheem

Comments

Popular posts from this blog

WANENE SHAIKH IBRAHIM ZAKZAKY (H) ???

DAGA GARIN KASUWAR GARBA DAKE JIHAR NEJA